1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

'Yan adawa sun soki rashin bin ka'ida a zaben Kwango

Zainab Mohammed Abubakar
December 20, 2023

A wannan Larabar ce aka gudanar da babban zabe a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, inda shugaba mai ci Felix Tshisekedi ke fafatawa da 'yan adawar da ke da rarrabuwar kawuna.

https://p.dw.com/p/4aQ52
Hoto: Paul Lorgerie/DW

Mai shekaru 60 da haihuwar ya kada kuri'arsa a babban birnin kasar watoKinshasa, biye da dumbin magoya bayansa da ke rera masa wakar yabo. Felix Tshisekedi ya yi shugabancin tsawon shekaru na ci gaban tattalin arziki amma akwai karancin ayyukan yi da hauhawar hauhawar farashin kayayyaki, a cikin kasar ta tsakiyar Afirka mai fama da talauci duk da arzikinta na ma'adinai.

An dai fuskanci rudanin gudanar da zaben saboda jinkiri, lamarin da ke tabbatar da fargabar cewa hukumar zaben ba ta shirya yin zaben ba, wadda tuni jam'iyyun adawa suka yi Allah wadan rashin bin ka'ida.

Sauran manyan 'yan takarar adawa sun hada da likitan kula da lafiyar mata Denis Mukwege mai shekaru 68, wanda ya lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel a shekarar 2018, da hamshakin dan kasuwa Moise Katumbi mai shekaru 58 kuma tsohon gwamnan lardin Katanga .