'Yan adawar Kamaru sun hade
October 6, 2018Talla
Wasu jam'iyyun adawa a Kamaru sun sanar da shirin dunkulewa waje guda, don ganin sun kwace mulki daga hannun Shugaba Paul Biya mai ci a babban zaben kasar da za a yi a ranar Lahadi.
Jagoran jam'iyyar FDP Akere Muna, ya janye daga takarar shugabanci da yake yi, don kara wa dan takara a jam'iyyar MRC Maurice Kamto karfin iya tinkarar Shugaba Biya mai shekaru 85.
Sai dai hadakar ba ta hada da dan takaran jam'iyyar SDF ba, wato Joshua Osih.
Ko a jiya Juma'a ma Maurice Kamto na jam'iyyar MRC, ya yi zargin ana tsara wani gagarumin magudi don bai wa Shugaba Biya damar zarcewa kan mulki karo na bakwai a Kamarun.
Jam'iyyar ta ce ana can ana ci gaba da rajistar masu zabe da aktunan boge a wasu wuraren, duk da cewar wa'adin rajistar ya shude.