Gangamin goyon bayan sojojin juyin mulki
August 3, 2023A Jamhuriyar Nijar, Alhaji Mahaman Ousmane tsohon shugaban kasar kana dan takarar da ya fafata da Bazoum Mohamed da zaben shugaban kasar da ya gabata, ya yi watsi da matakan takunkuman da kungiyar ECOWAS ta kargama wa Nijar da kuma shirin daukar matakin soja kann kasar domin tilasta wa sojojin mika matakin soja kan kasar domin tilasta wa sojojin mika mulki ga gwamnatin da suka hambarar. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da tawagar kungiyar ta ECOWAS ta isa birnin Yamai a kokarin samar da mafita a rikicin kasar.
A sanarwar da ya fitar Alhaji mahaman Ousmane tsohon shugaban kasar Nijar kana dan takarar da ya sha kayi a gaben Mohamed bazoum a zaben shugaban kasar da ya gabata, ya fara da nuna adawarsa da juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar, juyin mulkin da amma ya ce hukumomin jamhuriya ta bakwai ne suka zamo ummulhaba'isan afkuwarsa. Sai dai kuma ya nuna adawarsa da matakan kungiyar ECOWAS kann kasar inda ya yi karin bayani yana mai cewa.
Ya ce "A wannan hali da kasarmu ta shiga, nauyi ne da ya rataya a wuyana na jaddada adawata a bisa manufa da duk matakin kwatar mulki ta hanyoyin da suka saba wa doka da tsarin mulki. Amma yanzu lokaci ne da kamata mu hada kai , mu kuma nemi shawarwarin daga ciki da wajen kasar domin gaggauta mayar da kasar kann turbar demokradiyya a cikin wa'adi madaidaici. Sai dai ina mai adawa da duk wani yinkuri na amfani da karfin soja daga ketare kan kasar. Kazalika ina mai adawa da duk wani matakin takunkumi da aka saka wa kasar wanda ba abin da zai haifar illa kara jefa al'ummar kasar cikin mawuwacin hali baya ga wanda dama suke cikinsa tsawon shekaru 12 na mulkin wannan hanbararrar gwamnati".
Bayan kwan-gaba kwan baya na tsawon kwanaki, tawagar jami'an kungiyar ECOWAS a karkashin jagorancin Janar abdousalami abubakar da kuma mai martana sarkin muslmi na Sakkwato, Sa'ad Abubakar na uku ta iso a birnin Yamai inda za ta tattauna da sojojin kasar ta Nijar domin gano bakin zaren warware matsalar lokacin da y arage 'yan kwanaki wa'adin da kungiyar ta bai wa sojoji na su mika wuya su kuma mayar da mulki ga shugaba Mohamed bazoum, ko kuma jiki ya yi tsami.