1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan adawar Siriya ba za su je taron Sochi ba

Yusuf Bala Nayaya
January 27, 2018

Bangaren 'yan adawa a Siriya sun bayyana cewa ba za su halarci taron zaman lafiya ba da Rasha za ta jagoranta a mako me zuwa, kamar yadda me magana da yawun bangaren na adawa ya bayyana a wannan rana ta Asabar.

https://p.dw.com/p/2rbzK
Schweiz Syriengespräche in Genf | Staffan de Mistura & Nasr al-Hariri
Nasr al-Hariri jagoran 'yan adawa a Siriya daga dama na gaisawa da Staffan de Mistura Hoto: Getty Images/AFP/F. Coffrini

Yahya al-Aridi me magana da yawun 'yan adawar ya bayyana haka ne a karshen kwanaki biyu bayan tattaunawar da aka yi tsakanin bangaren gwamnatin ta Siriya da 'yan adawa karkashin sa ido na Majalisar Dinkin Duniya, wacce ta ce ba ta kammala shiri ba na ko za ta shiga taron da za a yi a Sochi ba.

Kasashen Yamma dai da wasu na Larabawa na kallon taron na Sochi a matsayin wani yunkuri na samar da shirin zaman lafiya da ka iya dusashe tauraron shirin MDD da ke neman kafa ginshiki na shirin da zai kawo zaman lafiya me dorewa a kasar ta Siriya baki daya, bayan kwashe shekaru na yakin basasa da ya jawo asarar dubu daruruwan rayuka na mutane da tilasta miliyoyi kauracewa muhallansu.