1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta bai wa 'yan Afghanistan mafaka

September 15, 2021

Ma'aikatar harkokin cikin gida ta Jamus ta ce ta bai wa 'yan Afghanistan kimanin 2,600 takardar izinin zama a kasar.

https://p.dw.com/p/40KzS
Deutschland | Afghanische Flüchtlinge landen mit dem letzten Flugzeug über Taschkent aus Kabul am Frankfurter Flughafen
Hoto: Kai Pfafenbach/REUTERS

Wadanda suka ci gajiyar mafakar sun hada da masu fafutukar kare hakkin dan Adam da masana kimiyya da fasaha da kuma 'yan jarida da ka iya fuskantar hatsari a Afghanistan din. Ma'aikatar ta kuma ce za a bai wa iyalansu izinin zama a Jamus ba tare da sun bi ka'idojin neman mafaka ba. Tun bayan da kungiyar Taliban ta kwace ikon Afghanistan a watan Augusta, gwamnatin Jamus ta ce fiye da mutane 4,500 ne jirgin rundunar kasarta ta Bundeswehr ya yi jigilar kwasowa daga Kabul. Mutanen sun hada da Jamusawa da kuma 'yan asalin Afghanistan da suka yi wa rundunar Bundeswehr aiki da kuma sauran cibiyoyin Jamus a kasar.