Yan Afrika a Iran da laifin safarar hodar ibilis
August 18, 2007Talla
Iran ta cafke wasu yan Africa 85 bisa laifin hada hadar hodar ibilis. A cewar shugaban hukumar yaki da miyagun kwayoyi na kasar, Hamid Reza,an cafke mutanen ne a wani sintiri da jami´an sa suka gudanar ne. Mr Reza yace mutanen sun hada da yan Nigeria da Ghana da kuma Tanzania. A cewar kwamandan , da yawa daga cikin mutanen na shigowa da hodar ta Ibilis ne daga Dubai, bayan sun hadiye ta a cikin cikin su izuwa kasar ta Iran.Bugu da kari Mr Reza ya kuma kara da cewa hukumar sa ta gano cewa wadannan mutane na amfani da kasar ne a matsayin wata cibiya ta rarraba wannan hoda, izuwa kasashen larabawa da kuma nahiyar Turai. Rataya da rai a cewar bayanai shine hukuncin mutumin da aka kama da hada hadar miyagun kwayoyi a kasar ta Iran.