'Yan Amurka biyu sun lashe kyautar Nobel ta likitanci
October 7, 2024Wasu masana kimiyya biyu na kasar Amurka Victor Ambros da Gary Ruvkun sun samu lambar yabo ta Nobel a fannin likitanci, bayan gano wani sabon nau'in kananan kwayoyin hallitu wadanda ke taka rawa wajen daidaita cututtuka. Ambros da ke da shekaru 70, masanin ilmin halitta ne a kwalejin kiwon kafiya na Massachusetts yayin da Ruvkun da ke da shekaru 72 ya kasance masani a fannin ilimin halittu a kwalejin kiwon Lafiya na Harvard.
Karin bayani: Pääbo ya samu Nobel ta fannin likitanci
Amurkawan biyu sun gudanar da bincike a kan wani nau'in tsutsa don sanin dalili da lokacin da kwayoyin halitta ke rikidewa, lamarin da ya ba da damar fadada gwaje-gwaje a kan cuttutuka da dama ciki har da ciwon daji da cututtukan koda na zuciya. Dama dai a bara, lambar yabo ta Nobel a fannin likitanci ta amince da ci gaba makamancin wannan da 'yar kasar Hungary Katalin Kariko da takwararta Drew Weissman na Amirka suka samar a fannin jirkita kwayoyin hallita na RNA wajen samar da allurar rigakafin Covid-19.