1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan aware sun kame gidan Talabijin a Ukraine

April 27, 2014

'Yan awaren Ukraine da ke goyon bayan Rasha sun kame wani gidan talabijin da ke Donesk a gabashin kasar, karon farko tun bayan da Ukraine din ta fada rikici na siyasa.

https://p.dw.com/p/1BpE8
Ukraine Masked pro-russischen Demonstranten
Hoto: picture-alliance/dpa

Wakilin kamfanin dillancin labarin AFP da ya shaida lamarin ya ce wasu mutane ne da dama sanye da kayan soji da kananan makamai suka yi wajen tsike, inda suka hana shige da fice a wajen kuma suka ce za su tabbata 'yan jarida da ke aiki a ciki na fadin gaskiya kamar yadda ya dace.

A wani labarin kuma 'yan awaren sun sako guda daga cikin jerin jami'an kungiyar nan ta tabbatar da tsaro da hadin kan Turai ta OSCE wanda suka kame a garin Slaviansk.

Masu aiko da rahotanni sun ce da ranar Lahadin nan ce 'yan awaren suka yi wa mutumin dan asalin kasar Sweden rakiya daga cikin wani gini da suke tsare da shi zuwa cikin wata mota kirar Jeep ta kungiyar ta OSCE da ke wajen ginin inda ya shige cikinta aka tafi da shi gida.

Mai magana da yawun shugaban 'yan awaren da ke Slaviansk Stella Khorosheva ta ce mutumin na fama da ciwon nan Diabetes ko Siga, wanda a cewarta shi ne ma ya sanya suka gadacewar sakinsa saboda dalilai na jin kai.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Usman Shehu Usman