'Yan aware sun samu nasara a Kataloniya
December 22, 2017Talla
Gamayyan jam'iyyun masu goyon bayan yankin Kataloniya ya balle daga kasar Spain sun samu nasara a zaben yankin da aka gudanar a wannan Alhamis da ta gabata. Jam'iyyu uku na 'yan aware sun samu kujerun majala 70, dama kujeru 68 ake bukata domin samun rinayje da ake bukata a wannan majalisa mai kujeru 135.
Tuni tsohon shugaban yankin na Kataloniya Carles Puigdemont wanda yake gudun hijira a Beljiyam ya ce sakamakon zabe ya zama kashedi ga mahukuntan Spain musamman Firaminista Mariano Rajoy, wadanda suka tunbuke shi daga madafun iko kuma suka kira zaben.