1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan awaren gabashin Ukraine sun yi alwashin kara dakaru

February 3, 2015

Yayin da Amirka ke tunanin bayar da makammai ga dakarun Ukraine, 'yan awaren gabashin kasar sun ce za su samar da dakaru akalla dubu 100 domin fuskantar abokan gaba.

https://p.dw.com/p/1EUlM
Hoto: Getty Images/AFP/A. Boiko

Sai dai kuma yayin da yake tsokaci kan wannan batu a wani taron manema labarai, jagoran 'yan awaren gabashin kasar ta Ukraine Alexandre Zakhartchenko ya ce su basa bukatar zubar da jini. Ya ce a shirye suke su dakatar da komai, muddin dai aka barsu da wuraren da ke hannunsu. 'Yan awaran dai sun samu mamaye wurare masu yawan gaske a gabashin kasar, tare da haddasa babbar asara a bangaren dakarun kasar ta Ukraine. Daga nashi bangare shugaban Rasha Vladimir Poutine, ya nuna damuwarsa kan wannan batu na gabashin Ukraine ganin yadda ake dada samun tada jijiyoyin wuya tsakanin bangarorin.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Mohammad Nasiru Awal