1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan bindiga sun kashe mutane 16 a Ituri

Mouhamadou Awal Balarabe
August 3, 2021

Fararen hula da dama sun gamu da ajalinsua lardin Ituri da ke gabashin Jamhuriyar Dimokradiyyar Kwango, a wani sabon hari da aka danganta da kungiyar 'yan tawayen ADF da ke da alaka da Yuganda.

https://p.dw.com/p/3yVCE
Milizsoldaten bewaffnete Gruppe URDPC/CODECO
Hoto: Alexis Huguet/AFP/Getty Images

Akalla fararen hula 16 ne aka kashe a lardin Ituri da ke gabashin Jamhuriyar Dimokradiyyar Kwango, a wani sabon hari da aka danganta da kungiyar 'yan tawayen ADF da ke da alaka da Yuganda. kungiyoyin farar hula na yankin sun bayyana cewar daga cikin wadanda rikicin ya rutsa da su, har da mata akalla biyu wadanda 'yan bindigan suka yi garkuwa da su.

 Gwamnan Lardin na Ituri wanda soja ne Laftanar-Janar Johnny Luboya Nkashama ya yi tir da kisan, inda a yayin wani gangami da ya gudanar a garin Komanda, ya yi alkawarin karfafa matakan tsaron don kare fararen hula.

An dade ana zargin ‘yan tawayen ADF na Yuganda da kisan gilla a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, inda suka kashe akalla mutane 6,000 cikin shekaru taran da suka gabata, a cewar wani rahoto da limamin cocin Kwango. Sannan kuma tun daga watan Afrilu na shekarar 2019,  kungiyoyai IS na daukar alhakin wasu hare-haren da 'yan tawayen ke kaiwa a yankin. kuma tuni Amirka ta sanya ADF a jerin "kungiyoyin 'yan ta'adda" masu alaka da IS.