1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwango ta sa dokar hana fita

Abdul-raheem Hassan
May 2, 2021

Harin ya faru bayan Shugaban kasar Felix Tshisekedi ya ayyana dokar hana fita a larduna biyu da aka samu asarar rayuka kusan 300 sakamakon rikicin kabilanci da yawaitar hare-haren 'yan bindiga.

https://p.dw.com/p/3sqp6
DR Kongo Provinz Ituri | MONUSCO- Friedenstruppen
Hoto: Alexis Huguet/AFP

'Yan bindiga dadi sun  kashe akalla mutane 19 ciki har da sojojin gwamnati 10 a wasu tagwayen hare-hare da suka kaddamar kan kauyuka biyu a gabashin kasar.

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya Unicef, ya ce rikici da ke faruwa a gabashin kasar ya tsananta halin rayuwa bayan tilasta sama da mutane miliyan daya da rabi gudun hijira, wasu miliyon biyu na cikin tsananin bukatar gajin gaggawa.