'Yan bindiga sun tayar da bam a Damaturu
February 15, 2015A cewar Adamu Muhammad da yake jawabi ga kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ji karar abin fashewa inda mutane suka watse. Sai dai ba shi da masaniya kan adadin wadanda abin ya shafa. A ranar Lahadi ne wani bam ya tashi a wata tashar mota mai cinkoson jama'a a garin Damaturu na jihar Yobe da ke yankin Arewa maso gabashin Najeriya.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da aka kama mutane da dama da ake ganin suna da alaka da kungiyar Boko Haram a kudancin Jamhuriyar Nijar sakamakon hare-haren da suke kaiwa a kasar. Kalla Moutari gwamna a Zindar ya fada wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa mutanen da ake zargin 'yan kasar ce ta Nijar .
An dai tura wadannan mutane zuwa birnin Niamey zuwa sashin da ke bincike kan masu ayyukan taaar da kayar baya don a gudanar da bincike a kansu . Kungiyar Boko Haram ta zafafa hare-harenta a yankin Diffa da ke da iyaka da Najeriya a 'yan kwanakin nan, abinda ya sanya mahukunta kara daukar matakai na tsaro.