'Yan ci rani 50 sun mutu a tekun Masar
September 22, 2016Masu aikin ceto a gabar tekun dai sun ce kawo yanzu sun kai ga ceto sama da mutane 163 sannan suka kuma gano gano wasu gawarwakin mutane tara a kan gawarwaki 41 da suka gano a farko, ciki har da wani dan yaro karami daga Masar da wasu 'yan Afirka takwas.
To sai dai haryanzu jami'an tsaro na ci gaba da binciken matuka jirgin hudu da aka kama da zargin wajen yunkurin kifar da jirgin, a tsakiyar mako ne dai jirgin ruwan ya nitse da daruruwan 'yan ci rani daga Masar, da Sudan da 'yan Somaliya da Äyan Siriya da iritiriya, a baya bayan dai tekun Massar na zama inda 'yan ci rani ke bi a kokarin su na tsallakwa kasashen turai.
A tun shekara 2014 ne dai akaluman Majalisar Dinkin Duniya ke nuna cewa mutane 10,000 ne suka yi asaran rayukansu a yunkurin su na subucewa zuwa kasashen Turai ta kogin Bahar-Rum.