'Yan damben Rasha za su kaurace wa gasar Olympics
July 6, 2024Bayan da aka haramta wa 'yan wasan Rasha shiga gasar sakamakon mamayar da Moscow ta kaddamar a Ukraine, a yanzu kwamitin shirya wasannin Olympic IOC ya bada dama ga wasu 'yan wasan kasar su fafata a gasar idan suka cika wasu tsattsauran ka'idoji da aka dauka, sai dai kuma 'yan wasan 10 da suka cike matakan su yi watsi da gayyatar.
Karin bayani: Zafi na barazana ga gasar Olympics a Paris
Hukumar ta ce, ba su amince da wasu ka'idoji na son rai ba da kwamittin ya gindaya ba, wajen zaben 'yan wasan da suka cancanta, inda a cewarta hakan ka iya raba kawunan 'yan wasanta.
'Yan wasan Rasha da ke fatan karawa a Olympics na bana da zai gudana a birnin Paris a bazarar bana, sai sun fito karara sun nisanta kansu da mamayar da Rasha ta kaddamar a Ukraine da kuma bayyana rashin alakarsu da dakarun kasar. Rasha dai ta yi sha yin watsi da manufar IOC.