'Yan gudun hijira dubu 13 a kan iyakar Girka
March 5, 2016A daidai lokacin da ya rage kwanaki biyu a bude taron koli na kasashen Turai da Turkiyya kan 'yan gudun hijira, rahotanni daga kasar Girka na cewa wasu 'yan gudun hijira kimanin dubu 13 sun tare a wannan Asabar kan iyakar kasar ta Girka da Masadoniya, inda suke zama a cikin wani munmunan halin rayuwa. Wani daga cikinsu ya yi tsokaci yana mai cewa:
"Ban san makomata ba, domin ba zan iya komawa baya ba, kuma ban samu damar tafiya gaba ba, don haka ban san yaya gobe za ta kasance ba. Watakila zan kwashe wata daya a nan ta yiwu ma karshen rayuwata ya kasance a cikin dakin tantin nan".
Dubban 'yan kasar ta Girka ne dai suka gudanar da zanga-zanga a wannan Asabar domin neman mahukunta su dauki matakan kyautata rayuwar 'yan gudun hijirar da ke jibge a kan iyakar kasar da Masadoniya. Wani daga cikin masu zanga zangar ya ce:
" Muna kira da a gaggauta sakin wadannan 'yan gudun hijira a kuma soke wannan sansani, sannan a samar masu gurin zama da ya dace da mutuncin dan Adam"
A ranar Litanin mai zuwa ce ake bude taron koli na shugabannin kasashen Turai da Turkiyya wanda ake yi wa kallon mai cike da mahimmanci a game da batun shawo kan matsalar kwararar 'yan gudun hijira zuwa Turai.