1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan gudun hijira na cigaba da shiga Turai

Ahmed SalisuSeptember 24, 2015

Dubban 'yan gudun hijira ne ke cigaba da shiga Turai daidai lokacin da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bukaci a magance abubuwan da ke sanya gudun hijira.

https://p.dw.com/p/1Gcd9
Flüchtlinge Österreich Bahnhof Ticket Schalter
Hoto: Alison Langley

Hukumomi a Hungary suka ce mutane sama da dubu goma ne suka shiga kasar ta cikin Croatia yayin da a Austria aka bada labarin shigar 'yan gudun hijira sama da dubu takwas a cikin sa'o'i talatin da shidddan da suka gabata.

Galibin mutanen da suka shiga kasashen dai sun fito ne daga Siriya wadda a yanzu haka ke fama da yakin basasa wanda ya yi sanadin rasuwar dubban mutane.

A wani taro da suka kammala dazu, shugabannin kasashen Turai sun amince da kara kudin tallafin da aka saba badawa ga kasashen da ke makotaka da Siriya a wani mataki na rage yawan wanda ke barin yankin don neman mafaka a Turai.