Kashe-kashen kabilanci a Sudan ta Kudu
June 9, 2023Sanarwar da hukumar bada agaji ta OCHA ta fitar ta nunar da cewa, mutuwar wani matashi dan kabilar Shilluk bayan da aka daba masa wuka ne ya kunna wutar rikicin a sansanin Malakal da ke tazarar kilomita 520 daga arewacin babban birnin kasar Sudan ta Kudu wato Juba. Wannan yanayi na rashin tsaro ya kawo cikas ga ayyukan jin kai, tare da haddasa dakatar da aikin jigilar 'yan gudun hijirar Sudan ta Kudu da ke tserewa rikicin Sudan.
Duk ma da kasancewarta 'yar auta a cikin kasashen duniya, amma Sudan ta Kudu na fama da rikice-rikicen siyasa da kabilanci da rashin zaman lafiya tun bayan samun ‘yancin kai daga Sudan a shekarar 2011. Ko da kafa gwamnatin rikon kwarya da aka yi bayan yakin basasa, bai hana tashe-tashen hankula ya ci gaba da zubar da jini a Sudan ta Kudu mai arzikin man fetur ba.