1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan gudun hijira sun kone matsuguninsu a Agadez

Tila Amadou
January 7, 2020

Hukumomi a Jamhuriyar Niger sun kama 'yan gudun hijira fiye da 300 bisa zargin tada bore da kona sansanin 'yan gudun hijirar da ke Agadez a arewacin kasar.

https://p.dw.com/p/3VrDl
DW - Global 3000 - Niger Flucht
Hoto: ZDF

A wani mataki na nuna rashin jin dadin su saboda dawo da su da akayi a sansaninsu 'yan gudun hijirar suka tada zanga zanga inda suka kone dakunan kwana kimanin 290 lamarin da ya tada hankalin mazauna garin na Agadez.

Abdourahmane Insar, daya daga cikin shugabnin kungiyoyin fararen hula a Agadez yace da ma ‘yan gudun hijirar suna da wata manufa

Jami'an tsaro sun kama 'yan zanga zangar
Jami'an tsaro sun kama 'yan zanga zangarHoto: Francesco Bellina

A halin da ake ciki an kama yan gudun hijirar da suka tada zanga zangar su kimanin 335 inda ake tsare da su, ana kuma cigaba da gudanar da bincike.

Amoumoun Aghali  jami’i  a majalisar mashawart ta , ta jihar Agadez ya yi kira ga mahukunta su dauki mataki.

Shougabar hukumar kula da ‘yan gudun hijira a Niger Alessandra Morelli  ta kai ziyara jihar Agadez  don duba girman matsalar inda za ta zauna da hukumomin Agadez don neman mafita.

Garin Agadez ya zama babbar hanyar da yan gudun hijira daga yankin hamadar Afirka ke ratsawa a yunkurinsu na zuwa kasashen Turai a waje guda kiuma da wadanda ke gujewa tashin hankalin da ke gudana a makwabciya kasar Libya.