1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan gudun hijirar Ukraine sun kai miliyan 2

March 8, 2022

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce adadin 'yan gudun hijirar Ukraine sun kai miliyan biyu, adadi mafi girma tun yakin duniya na biyu.

https://p.dw.com/p/48B6O
Ukraine-Krieg | Flucht aus Irpin bei Kiew
Hoto: DIMITAR DILKOFF/AFP

Shugaban hukumar Filippo Grandi ya ce ta yiwu kashi na biyu na kwarara 'yan gudun hijirar daga Ukraine din ya ninka na farko da ake gani a yanzu. Kawo yanzu dai fiye da 'yan gudun hijira miliyan daya suka tsallaka kasar Poland.

Kwamitin ceto na kasa da kasa (IRC) ya shaida cewa barnar da yaki ya haifar a Ukraine na bukatar hanyoyin jinkai na dogon lokaci don magance kwarara 'yan gudun hijirar.

Tuni dai kasar Japan ta sanar da shirinta na karbar wasu jerin 'yan gudun hijirar zuwa kasarta.