Kokari tsallaka iyaka ta karfi zuwa Spain
December 25, 2015Wasu 'yan gudun hijira daruruwa daga Afirka sun farwa yankin Ceuta da ke iyakar Moroko da kasar Spain a kokarin kutsa kai kasar, yunkurin da ya jawo sanadi na rayuwar 'yan gudun hijira biyu wasu goma sha biyu aka garzaya da su asibiti kamar yadda jami'ai daga dukkanin bangarorin biyu suka bayyana.
Wannan lamari dai ya faru ne da misalin karfe uku agogon GMT a kusa da yankin Benzu a Arewacin na Ceuta inda masu mutanen ke kokari su tsallaka wayar da aka girka a matsayin shinge na hanasu tsallakawa ko kuma su bi ta ruwa suna iyo har zuwa gabar ruwa da za ta sada su da wannan birni.
Kimanin 'yan gudun hijirar 200 ne dai suka yi wannan yunkuri na tsallaka iyakar ta hanyar yin iyo ta teku daga Arewacin na Maroko a cewar kamfanin dillancin labarai na MAP. Mahukuntan kasar ta Moroko sun sami damar tattara mutane 104 da tun dafari a kan iyaka suka yi amfani da sandina da duwatsu wajen afkawa jami'an tsaro yayin da ita kuma kungiyar Red Cross a yankin na Ceuta ta ce ta kula da lafiyar mutane da dama da suka samu damar tsallakowa.