1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Iraki sun agaza domin kwato Ramadi

Gazali AbdouMay 18, 2015

Mayakan 'yan shi'a na kasar Iraki na shirin kwato birnin Ramadi daga hannun mayakan kungiyar jihadi ta IS bayan da hukumomin Kasar Iraki suka nemi agaji

https://p.dw.com/p/1FRYM
Irak Kämpfe um Ramadi
Hoto: picture alliance/AP Photo

Hukumomin kasar Iraki sun juma suna wasuwasin neman daukin mayakan kungiyar 'yan shi'an a cikin wannan yaki.Sai dai kwace birnin Ramadi ya kasance wani babban komabaya ga kasar ta Iraki, abunda ya sanya hukumomin kasar suka yanke shawarar karbar tayin mayakan 'yan shi'an.

Yanzu haka dai tarin motocin yakin mayakan 'yan shi'a ne suka kama hanya zuwa filin daga domin dafawa sojojin gwamnatin a wannan yinkuri na neman kwato birnin na Ramadi wanda ya fada hannun mayakan kungiyar 'yan jihadin ta IS.

Kungiyar mayakan 'yan shi'a ta ce fadawar birnin Ramadi a hannun mayakan kungiyar IS wata shaida ce da ke nuni da cewa dole sai an yi taron dangi, an manta da duk wasu banbance- banbancen akida domin kare tare da ceto yankunan kasar Irakin da suka kubucewa milkin Bagadaza