'Yan Isra'ila uku da Hamas ta sako sun isa gida
January 19, 2025Da yammacin wannan Lahadi sojojin Isra'ila sun sanar da cewa mutane uku daga cikin wadanda Hamas ta yi garkuwa da su sun isa cikin kasar, kamar yadda yarjeneiyar tsagaita wuta a Gaza wadda ta fara aiki a safiyar lahadi ta tanadar.
Gidan talabijin din Isra'ila ya ruwaito kakakin rundunar sojin kasar na cewa mutanen uku da suka hada da Emily Damari da Romi Gonen da kuma Doron Steinbrecher sun tsallaka iyakar kasar daga yankin Falasdinu kuma a halin yanzu suna kan hanyar isa ga iyalansu, tare da bayyana lamarin a matsayin lokaci na murna.
Karin bayani: Yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta fara aiki
Shugaban Amurka mai barin gado Joe Binden ya yi maraba da wannan mataki da aka kai a karkashin yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas a Gaza wanda ke zuwa a ranar karshe ta wa'adin mulkinsa, sannan kuma ya karfafa fatan dorewarta don kawo karshen zubar da jini a dan karamin yankin na Falasdinu.
Daga nata bangare shugabar hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta ce sakin wadannan 'yan Isra'ila uku domin komawa cikin iyalansu abu ne na farin ciki da ke nuna alamun yarjejeniyar za ta dore.