Ranar 'yancin 'yan jarida ta duniya
May 3, 2020Rahoton kungiyar kare hakkin jama'a ta kasa da kasa ta Amnesty International data wallafa a wannan Lahadi ya nunar da haka.
A dai dai lokacin da yawan wadanda suka kamu da cutar Coronavirus ke karuwa, gwamnatin masar na kara tsananta ikonta kan toshe hanyoyin samun bayani, maimakon barin duniya ta san gaskiyar halin da ake ciki game da lafiyar al'umma, a cewar kungiyar Amnesty mai matsugguni a birnin London.
Tuni dai hukumomin kasar suka yi gargadin cewar, duk dan jaridan da ya kalubalanci bayanan gwamnati, zai fuskanci hukunci mai tsanani, a cewar Philip Luther, darektan kungiyar na yankin Gabas ta Tsakiya da yankin Arewacin Afirka.
Amnesty ta bada misallin 'yan jarida 37 da a yanzu haka ke tsare, a kan zargin abun da gwamnatin Masar din ta kira " Yayata bayanan karya ko kuma saba ka'idojin amfani da shafukan sada zumunta na zamani".