1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tashar DW ta karrama 'yan jarida biyu daga UKraine

June 21, 2022

Tashar DW ta mika kyautar fadin albarkacin baki ga 'yan jaridar Ukraine guda biyu domin karrama jarumtarsu wurin fara bayar da rahotannin yadda rikicin Ukraine ya fara ragargaza birnin Mariupol.

https://p.dw.com/p/4D1wr
GMF 2022 | Kyautar jaruntaka kan aikin jarida | Wadanda suka samu Mstyslav Chernov da Evgeniy Maloletka
'Yan jarida da suka samu kyauta Mstyslav Chernov da Evgeniy MaloletkaHoto: Florian Görner/DW

Tashar DW ta mika kyautar fadin albarkacin baki ga 'yan jaridar Ukraine guda biyu domin karrama jarumtarsu wurin fara bayar da rahotannin yadda rikicin Ukraine ya fara ragargaza birnin Mariupol. An karrama 'yan jaridar dai ne a wurin wani kasaitaccen biki da aka yi birnin Bonn na Jamus a taron 'yan jarida na duniya da DW ke shiryawa shekara-shekara da aka fi sani da Global Media Forum.

Jami'in da ya jagoranci gabatar da kyautar ta fadin albarkacin bakin ya kwashe tsawon lokaci yana tulawar irin jarumar da 'yan jaridar suka nuna wurin bayar da rahotannin yakin Ukraine, mahalarta wannan taro kuma sun rika tafi domin mutunta kwazon da 'yan jaridar suka nuna.

Karin Bayani: GMF na neman kyautata aikin jarida a duniya

GMF 2022 |Kyautar 'yancin albarkacin baki | Wadanda suka samu nasara
Kyautar 'yancin albarkacin baki Hoto: Ronka Oberhammer/DW

'Yan jaridar biyu dai wadanda 'yan salin kasar Ukraine ne su ne Mstyslav Chernov da abokin aikinsa  Evgeniy Maloletka. Duk suna aiki ne a kamfanin dillancin labarai na Associated Press.

'Yan jaridar dai sun samu damar gudanar da wannan aiki da ya bai wa duniya mamaki ne biyo bayan nan nasarar da suka yi ta shiga birnin na Mariupol 'yan sa'o'in kafin dakarun Rasha su fara harbo makamai masu linzami a birnin. Haka suka kwashe makonni uku cur suna aikin cikin tashin hankali. Shugabar kwamitin CPJ mai kare muradun 'yan jarida a duniya Sally Buzbee wacce ta jinjina wa 'yan jaridar ta ce kawo yanzu kusan 'yan jarida 12 ne aka tabbatar da kashewa a yakin Ukraine.

Shugaban tashar DW Peter Limbourg ya yi jawabi ga mahalarta taron cikin jimami, bayan da ya kalli cikakken bidiyon farko na barnar da aka fara yi yakin na Ukraine wanda aka kunna a wurin taron, ya kusan fashewa da kuka, inda idanunsa cike da kwalla.

GMF 2022 | Kyautar 'yancin albarkacin baki | Wadanda suka smau nasara
Kyautar 'yancin albarkacin bakiHoto: Philipp Boell/DW

Ba domin bidiyo mai cike da hujjoji na yankan shakku da 'dan jarida Chernov da abokin aikinsa Maloletka suka fitar ba, da an dauki lokaci mai tsawo kafin duniya ta fahimci girmin barin wutar da Rasha ta fara yi a Ukraine a watan Fabrairu. 'Yan jaridar sun nuna wagegen ramin da aka rufe gawawwakin fararen hula da yadda cikin tsananin hunturu dakarun Rasha suka katse makamashin iskar gas da lantarki daga gidajen mazauna Mariupol, lamarin da ya jaza rashin ruwan sha da abinci wurin na makonni uku a birnin.

'Yan jaridar dai ba sabbi ba ne wurin bayar da rahotannin yaki. Kafin yanzu sun aiko rahotanni daga fagen daga a Siriya da Iraki da kuma Myanmar. A yayin da DW ke karrama su a wannan Litinin, Chernov da Maloletka sun lashi takobin komawa Ukraine domin ci gaba da bayar da rahotannin halin da ake ciki ba tare da tsoro ko fargaba ba.