'Yan kabilar Uighur na zanga-zanga a Turkiyya
March 25, 2021Talla
Zanga-zangar na zuwa ne a daidai lokacin da ministan harkokin wajen kasar Chaina Wang Yi ke wata ziyarar aiki a birnin Ankara.
Beijing na mai muradin kaddamar da musayar fursunoni a tsakanin kasashen biyu da zai ba da damar maida wasu 'yan kabilar ta Uighur zuwa Chaina. Sai dai al'umma da kungiyoyin kare hakkin bil'Adama da ma wasu 'yan kabilar sama da mutum dubu 40 sun nuna damuwarsu a kan alakar da kasar ke shirin kullawa da mahukuntan na Beijing.
Ministan harkokin wajen Turkiyya ya ce a wannan ziyara ta takwaransa akwai batutuwa da dama da za su tattauna, kuma a
gaba, ana sa ran ganawar ministan na Sin da shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan.