1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

'Yan kasashen waje na ficewa daga Lebanon

Abdullahi Tanko Bala
October 3, 2024

Baki 'yan kasashen waje daga Turai da nahiyaar Asiya da kuma Gabas ta Tsakiya na ficewa daga Lebanon a yayin da Israila ke ci gaba da luguden bama bamai a Beirut

https://p.dw.com/p/4lNho
Lebanon | Filin jirgin saman Beirut cike da masu son ficewa daga Lebanon
Hoto: Houssam Shbaro/Anadolu/picture alliance

Yan kasashen waje daga Turai da nahiyaar Asiya da kuma Gabas ta Tsakiya na ficewa daga Lebanon a yayin da Israila ke ci gaba da luguden bama bamai a Beirut babban birnin kasar. A waje guda dai gwamnatoci a fadin duniya sun bukaci yan kasashensu su fice daga Lebanon.

Wasu kasashen sun samar da jirage domin kwashe mutanensu a wasu wuraren kuma daruruwa mutane na shiga jiragen ruwa da kananan kwale kwale domin ficewa.

Israila ta bukaci jama'a su kauce daga garuruwa fiye da ashirin a kudancin Lebanon a ci gaba da rikicin da ya ja Iran shiga ciki da kuma barazanar fadawar Amurka cikin rikicin.