1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Taron goyon bayan juyin mulki

August 6, 2023

Dubban mutane a Nijar sun gudanar da taron nuna goyon baya ga juyin mulki da aka yi a kasar yayin da ake daf da cikar wa'adin da ECOWAS ta ba sojoji na su koma bariki.

https://p.dw.com/p/4Upzj
Masu goyon bayan juyin mulki a Nijar
Masu goyon bayan juyin mulki a NijarHoto: Mahamadou Hamidou/REUTERS

Sama da mutane dubu 30 sun gudanar da wani gagarumin taro a babban filin kwallon kafa na birnin Yamai fadar gwamnatin Nijar, domin jaddada goyon baya ga sojojin da suka hambarar da shugaba Mohamed Bazoum.

Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ruwaito cewa, tawagar majalisar sojojin karkashin Janar Mohamed Toumba ta halarci toron domin nuna wa duniya karbuwar da juyin mulkin ya samu daga 'yan kasar. Yayin da yake jawabi a gaban dandazon jama'ar da ta cika filin kwallon dauke da tutocin kasar da kuma na Rasha, Janar Mohamed Toumba ya soki aniyar masu son yin katsalandan a kan sabuwar turbar ci-gaba da ya ce majalisar ta CNSP ke son dora Nijar din a kai.  

Taron na wannan Lahadi da ba a taba ganin irinsa ba tun bayan juyin mulki a ranar 26 ga watan Yuli, na zuwa ne a daidai lokacin da sa'o'i kadan suka rage a kai ga cikar wa'adin da kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Kasashen Afrika ta Yamma ECOWAS ta bai wa sojojin na su dawo da hambararren shugaban kasar kan kujerarsa ko kuma ta yi amfani da matakin soja domin kawar da su.