1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan sanda a Masar sun tarwatsa masu zanga-zanga

Gazali Abdou tasawaAugust 14, 2015

Masu zanga-zangar na tunawa da ranar zagayowar shekaru biyu da kisan ɗaruruwan masu zanga zangar nuna adawa da tsige Mohamed Morsi da sojoji suka yi daga kan milki

https://p.dw.com/p/1GFq6
Zusammenstöße zwischen Muslimbrüdern und Sicherheitskräften in Kairo
Hoto: el-Shahed/AFP/Getty Images

A ƙasar Masar a wannan Jumma'a 'yan sanda sun yi amfani da barkonon tsohuwa da kulake domin tarwatsa magoya bayan tsohon Shugaban ƙasar Mohamed Morsi waɗanda suka yi yinƙurin shirya taron gangami na tunawa da ranar zagayowar shekaru biyu da kisan gillar ɗaruruwan jama'a da jami'an tsaron ƙasar suka yi lokacin wata zanga-zanga da magoya bayan tsohon shugaban ƙasar Morsi suka shirya a filayen Rabaa Al-Adawiya da na Al-Nahda na cikin birnin Alƙahira domin nuna adawarsu da matakin tsige shugaban daga kan karagar milki da sojojin ƙasar suka yi a ranar 3 ga watan Yulin shekara ta 2013.

Kungiyar kare hakkin Ɗan Adam ta kasa da kasa ta Human Rights Watch a wannan JumMa'a ta yi kira ga MDD da ta gudanar da bincike akan wannan batu wanda ta bayyana a matsayin kisan gillar masu zanga-zanga mafi muni a tarihin wannan zamani.