1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaKenya

Kenya: 'Yan sanda na murkushe zanga-zanga

Lateefa Mustapha Ja'afar
July 16, 2024

Jami'an 'yan sanda a Kenya sun harba barkonon tsohuwa a kan dandazon masu zanga-zanga da ke neman Shugaba William Ruto ya sauka daga mukaminsa a Nairobi babban birnin kasar.

https://p.dw.com/p/4iNQy
Kenya | Nairobi | Zanga-Zanga | Adawa | William Ruto
Jami'an tsaro na murkushe masu zanga-zanga da karfin tuwo a KenyaHoto: TONY KARUMBA/AFP/Getty Images

Tsawon wata guda ke nan da masu fafutuka karkashin jagorancin Gen-Z Kenyans suka kaddamar da zanga-zangar ta rikide zuwa tashin hankali da kuma yin sanadiyyar rayuka da dama, sakamakon karin kudin haraji da gwamnati ta yi. Zanga-zangar dai ta tilasta Shugaba William Ruto na Kenyan ajiye kudirinsa na karin harajin, sai dai duk da haka masu zanga-zangar na ci gaba da matsin lamba na ganin tilas sai ya sauka daga mukaminsa.