1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan sanda sun gano sama da bama-bamai dari a birnin Kano

January 23, 2012

A birnin Kano dake Tarayyar Najeriya yan sanda sun gano motoci takwas makare da bama bamai, abinda ke nuna irin barazanar da har yanzu birnin ke fiskanta, tun bayan tashin bama-bamai da ya hallaka jama'a da yawa a birnin

https://p.dw.com/p/13obq
A rescue worker inspects the burnt-out wreckage of cars and motorcycles destroyed by multiple explosions and armed assailants in the Marhaba area of the northern Nigerian city of Kano, on January 21, 2012. Coordinated bomb attacks on January 20 targeting security forces and gun battles have killed at least 121 people in Nigeria's second-largest city of Kano, with bodies littering the streets. AFP PHOTO / AMINU ABUBAKAR +++(c) dpa - Bildfunk+++
Nigeria Kano BombenanschlagHoto: picture-alliance/dpa

Duk da cewar harkokin kasuwanci sun dawo ka'in da na'in a jihar Kano, amma dai mutane na cikin fargaba da rudani, musamman ganin yadda yawancin caji ofis din yan sanda suke a rufe da kuma yadda ake ci gaba da samun motoci makare da bama bamai awasu sassan jihar.

Tun bayan hare-haren da kungiyar Jama'atul Ahalu Sunna Lidda'awati Waljihad ta kawo a birnin Kano, ranar Juma'ar da tagabata, inda mutane da dama suke cikin fargaba da rudani. Koda yake dai zuwa yanzu mutane na cigaba da gabatar da harkokinsu na kasuwanci da aikace-aikace, amma dai kowa yana cikin dardar, musamman ganin yadda aka samu bacewar yan sanda a sassa daban daban, yawancin caji ofis caji ofis a birnin a rufe suke.

A truck carrying victims of a bomb attack is parked in front of a mortuary in Nigeria's northern city of Kano January 21, 2012. More than 100 people were killed in bomb attacks and gunfights in Nigeria's second largest city Kano late on Friday, a senior local government security source told Reuters, in the deadliest coordinated strike claimed by Islamist sect Boko Haram to date. REUTERS/Stringer(NIGERIA - Tags: CRIME LAW RELIGION)
Masu aikin agajin gaggawa bayan harin birnin kanoHoto: Reuters

Yanzu haka dai sojoji ne suke kula da tsaro a titunan birnin na Kano, haka kuma dukkan hanyoyin zuwa manyan ofisoshin yan sandan jihar a rufe suke, lamarin da ya haddasa cunkoson ababan hawa.

Har ila yau kuma an ci gaba da samun karin wasu motoci makare da bama bamai, bayan da aka samu wasu motoci 2 a gidan man Mega Station dake Hotoro da tsakar ranar yau kuma, aka sake samun wasu motocin makare da bama-bamai, ko da yake dai bama-baman ba su kai ga tashi ba, amma dai dukkan mutanen dake kusa da wurin sun kauce domin tsoron abin da zai je ya zo, yan sanda dai ba su ce komai ba akan wannan batun na kama motocin.

Da yammacin yau ne ake sa ran wani taro tsakanin hukumomin lafiya da na kungiyoyin agaji, dama wakilan gwamnatin tarayya, domin tattauna wannan alamari, haka kuma a yau gwamnatin Kano da fadar mai martaba sarkin Kano, suka gabatar da addu'o'i na musamman a masallacin Juma'a na fadar sarki, domin dai rokon Allah ya kawo karshen wannan matsalar.

Nigerian police officers stand guard in an area were the military are battling with gunmen in Kano, northern Nigeria, Wednesday April 18, 2007. Security forces in northern Nigeria battled gunmen blamed for a deadly attack on a police station a day earlier, with gunfire erupting around dawn Wednesday and witnesses reporting casualties. Hundreds of soldiers and police surrounded the area as entire families fled. The violence in Kano has added to tension across Africa's most populous nation days before a presidential vote meant to usher in the first civilian-to-civilian transfer of power in a nation whose history since independence in 1960 has been plagued by military coups. (AP Photo/George Osodi)
Jami'an yan sandan NajeriyaHoto: AP

Wata majiyar yan sanda ta fadawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, kawo yanzu sun gano sama da bam-bamai 100 a birnin na Kano, tun bayan tashin hankalin da rutsa da birnin a ranar Juma'a da ta gaba.

Mawallafi: Nasiru Salisu Zango

Edita:       Usman Shehu Usman