1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa: Arangama a yayin bikin Bastille

Ramatu Garba Baba
July 14, 2019

A wannan Lahadi aka gudanar da kasaitaccen bikin tuni da juyin-juya hali na Bastille da aka saba yi duk ranar 4 ga watan Yulin kowacce shekara, amma zanga-zanga ta ragewa bikin armashi.

https://p.dw.com/p/3M4Og
Frankreich | Gelbwestenproteste am Nationalfeiertag
Hoto: Getty Images/AFP/K. Tribouillard

Kamar yadda aka saba a kowace shekara an soma bikin da faretin soji. Sai dai bikin na bana ya zo da matsala a sakamakon arangama a tsakanin jami'an tsaro da masu zanga-zangar adawa da shirin gwamnati na kara harajin farashin mai wadanda suka yi dandazo a harabar fadar gwamnati ta Elysees.

Shugaba Emmanuel Macron ya yaba da hadin kan rundunar sojin Turai a yayin jawabinsa. Duk da cewa hargitsin ya ragewa bikin na bana armashi, an ci gaba da bikin da ya sami halatar Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel da wasu wakilai na kasashe mambobi a kungiyar Tarayyar Turai EU.