'Yan sanda sun tsare masu bore a Hong Kong
November 18, 2019Talla
Rahotanni daga yankin Hong Kong na cewa 'yan sanda sun fesa hayaki mai sa kwalla tare da watsa ruwa zafi kan daruwan masu zanga-zanga da ke neman tserewa daga wata wata kwaleji, an dade ana zargin jami'an tsaron gwamnati na amfani da karfi kan masu boren, sai dai suna samun kariya daga gwamnati.
Wannan dai na zuwa a dai-dai lokacin da wata kotu a yankin na Hong Kong ta soke haramcin da aka yi na rufe fuska dan badda kama yayin gudanar da zanga-zangar neman 'yancin cin gashin kai daga gwamnatin Beijin.