1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

'Yan sandan Guinea sun yi arangama da masu bore

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
March 18, 2024

Matasan sun datse hanyoyi da kona tayoyi, tare da jifan 'yan sandan da duwatsu, yayin da su kuma 'yan sandan suka rinka harba musu hayaki mai sa hawaye don tarwatsa su

https://p.dw.com/p/4aSyL
Hoto: Youssouf Bah/AP/picture alliance

'Yan sanda a birnin Conakry na kasar Guinea sun yi arangama da matasa da ke zanga-zangar bukatar ganin an dawo da sayar da man fetur a gidajen man yadda aka saba, bayan dakatar da sayarwar a dalilin gobarar da ta tashi a babbar cibiyar rarrabar man fetur din kasar.

Karin bayani:Gobara a cibiyar tattara man fetur din Guinea Conakry ta hallaka mutane 11

Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya rawaito cewa a jiya Alhamis matasan sun datse hanyoyi da kona tayoyi, sannan suka rinka jifan 'yan sandan da duwatsu, yayin da su kuma 'yan sandan suka rinka harba musu hayaki mai sa hawaye don tarwatsa su.

Karin bayani:Siyasar Guinea ta dagule

A ranar Litinin din da ta gabata ne dai gobara ta tashi a babbar cibiyar tattarawa tare da raba man fetur din kasar ta kasar Guinea da ke Conakry babban birnin kasar, wadda ta yi sanadiyyar asarar rayukan mutane 23, tare da jikkata 241.