'Yan sandan Yuganda sun kama Bobi Wine
April 29, 2019Jami'an 'yan sandan Yuganda sun sake cafke dan gwagwarmayar nan Bobi Wine sa’o’I 48 bayan dan adawan ya samu 'yancinsa na walwala da zirga-zirga. Masu aiko da rahotanni sun ambato lauyan Bobi Wine na cewa “tun da sanyin safiya ne ‘yan sanda suka kamashi tare da tsareshi a wani ofishin ‘yan sanda da ke wajen birnin Kampala ba tare da bayyana dalilan da suka haddasa kamunsa ba. "
Dan shekaru 37 da haihuwa, mawakin Bobi Wine ya yi kaurin suna wajen caccakar masu zartar da mulki a kasar Yuganda wanda har ma matasan kasar suke daukarsa a matsayin wani jagoran juyin-juya hali domin isar da sakonsu ga mahukunta, Si dai tun a ranar 23 ga wannan watan aka girke jami’an ‘yan sanda a gaban kofarsa tare da hana hi duk wani motsin da ya shafi shige da fice.