Yan Siyasa a Girka sun cimma yarjejeniya
February 9, 2012Shugabar asusun ba da lamuni ta duniya christine lagarde ta yaba da yarjejeniyar da ƙawancen jam'iyyun siyasa masu yin mulki a ƙasar Girka suka cimma na amincewa da wasu ƙarin matakan tsuke bakin aljihun gwamnati.
christine lagarde wacce ta baiyana haka a birnin Brussels inda ta ke halarta taron ministocin kudi na ƙasashen ƙungiyar Tarrayar Turan ta ce ƙarin matakan da aka buƙaci ƙasar Girka ta ƙaddamar zai ba ta damar samu wani sabon rance na hukumar IMF kimanin biliyan dubu 130.To sai dai ministan kuɗi na ƙasar Holland ya ce taron ministocin ba zai iya yanke hukumci ba da tallafin ba ga ƙasar Girka du da ma yarjejeniyar da suka cimma.An dai ƙwashe ƙwanaki ana samun saɓannin ra'ayoyi akan shirin tsakanin jam'iyar Pasok ta masu neman sauyi da kuma jam'iyyar masu tsatsaura ra'ayi akan matakan da yawancin al'ummar ƙasar suke nuna adawa da su.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Ahmad Tijani Lawal