Geneva: Kokarin warware rikicin siyasar Chadi
October 23, 2019Talla
Tun dai bayan zaben shugaban kasa na 2016 wanda Shugaba Idriss Deby ya lashe a karo na biyar, Chadi ta fada cikin rigingimun siyasa. Ana cikin wannan yanayi ne a shekara ta 2018 gwamnatin kasar ta bi ta hanyar majalisar dokoki ta sabunta kundin tsarin mulkin kasar wanda ya tanadi karin karfin iko ga shugaban Idriss Deby. Lamarin da ya kara zafafa yanayin siyasar kasar da yin illa ga tattalin arzikinta. Kungiyar Utopie Nord-Sud ta Chadi ce dai ta kira wannan taron tattaunawa wanda a tsawon kwanaki biyu zai yi kokarin tantance illahirin matsalolin da Chadi ke fama da su da kuma samar da mafita, da zimmar maido da zamna lafiya da kwanciyar hankali a kasar. Sai dai kuma gwamnatin ta Chadi ba ta halartar taro.