'Yan siyasar Nijar sun ce sai an dawo da Bazoum
July 27, 2023A wata hira ce da kakakin jam’iyyar PNDS Tarayya mai mulki Malam Iro Sani ya yi da tashar DW a safiyar wannan Alhamis, ya tabbatar da matsayin jam’iyyar tasu na yin watsi da juyin mulkin da sojojin suka yi.
Wannan na zuwa ne a daidai loakcin da sojojin da suka yi juyin mulki ke ci gaba da fitar da sanarwoyi da suka hada da na dakatar da duk wasu ayyukan jam’iyyun siyasa a Nijar.
Kakakin jam’iyyar ta PNDS Tarayya ya ce duk da ikirarin da sojojin suka yi na karbar mulki, jam’iyyarsu na da sauran lakonta, kuma za ta yi gwagwarmayar maido da shugaba Mohamed Bazoum kan kujerarsa.
Ya zuwa yanzu dai a hakumance kawancen jam’iyyun adawar kasar wanda ya jima yana kalubalantar gwamnatin ta Shugaba Bazoum Mohamed, ba ta bayyana matsayinta a kan juyin mulkin ba. Sai dai Malam Kane Habibu Kadaoure, shugaban jam’iyyar adawa ta SDR Sabuwa ya ce ko da yake ba su ji dadin abin da ya faru ba amma dai sun san a rina.
Daga nasu bangare dai kwamitin sojojin da suka yi juyin mulki ya tabbatar da Janar Omar Tchani a matsayin shugaban majalisar kiyaye zaman lafiya ta kasa ta CNSP, sannan suna ci gaba da fitar da jerin sanarwoyi da matakai da suka tsara tare da dakatar da duk ayyukan jam’iyyun siyasa, gami da yin kashedi ga kasar Faransa a game da keta dokar rufe iyakokin sama na kasar, sannan ta ce illahirin sauran manyan sojojin kasar sun yi mubaya’a ga sanarwa da majalisar sojojin juyin mulki ta CNSP ta fitar.