1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan ta'adda a Siriya sun yi garkuwa da mata da kananan yara

Mohammad Nasiru Awal SB
July 30, 2018

Sama da mutum 250 aka kashe a hare-haren da mayakan kungiyar 'yan ta'adda suka kai a shalkwatar lardin Suwaida da kauyukan da ke kewaye a ranar Laraba da ta gabata.

https://p.dw.com/p/32Jcv
Syrien al-Qaida in Aleppo
Hoto: picture-alliance/Pacific Press/I. Khader

A lardin Suwaida da ke kudancin kasar Siriya, mayakan kungiyar 'yan ta'adda ta IS sun yi awan gaba da mata da kananan yara 36 a makon da ya gabata. Kungiyar sanya ido kan hakkin dan Adam a Siriya ta sanar cewa akalla mata 20 da kananan yara 16, dukkansu mabiya addinin tsiraru na Drusen aka yi garkuwa da su a makon da ya gabata.

Ita ma kafa watsa labaru ta yankin wato Soueida24 ta ba da labarin sace mutanen.

Mutane fiye da 250 aka kashe a jerin hare-haren da mayakan kungiyar 'yan ta'adda suka kai a shalkwatar lardin Suwaida da kauyukan da ke kewayenta a ranar Laraba da ta gabata.