An kai wa sansanonin sojan Mali hare-haren ta'addanci
March 16, 2024Talla
A cikin wata sanarwar da ta fitar, ma'aikatar tsaron Mali, ta ce an kai jerin hare-haren ne kan wasu sansanonin sojoji biyu da kuma wani shingen binciken jami'an Custom da ke wani kauye mai tazarar kilo mita akalla 100 daga kudancin birnin Bamako.
Sai dai rundunar tsaron kasar ta ce dakarunta sun yi nasarar fatattakar maharan, tare da kashe da dama daga cikinsu, kana kuma rundunar ta kara da cewa da dama daga cikin 'yan ta'addan sun samu mafaka a wani kungurmin daji.