1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

'Yan ta'adda sun kashe mutane 10 a Manni na Burkina Faso

Mouhamadou Awal Balarabe
October 8, 2024

Rundunar sojin Burkina faso ta tabbatar harin, inda da ce dakarunta sun kai farmaki a yankin don tinkarar 'yan ta'ada, ba tare da wani karin bayani kan adadin mace-mace ba.

https://p.dw.com/p/4lXOr
Hare-haren Burkina Faso na afkuwa a Ouagadougou da sauran biranen kasa
Hare-haren Burkina Faso na afkuwa a Ouagadougou da sauran biranen kasaHoto: Getty Images/AFP/A. Ouoba

Akalla fararen hula goma sun mutu a wani harin da masu kaifin kishin addini suka kai a wata kasuwa da ke garin Manni a yankin Arewa maso gabashin Burkina Faso. Wasu majiyoyin yankin da suka kwarmata labarin, suka ce harin da ya auku a ranar Lahadi ya jikkata mutane fiye da hamsin da ke kwance yanzu haka a asibiti.  Ita ma rundunar sojin Burkina faso ta tabbatar da cewa dakarunta sun kai farmaki a yankin don karya lagon 'yan ta'ada, ba tare da wani karin bayani kan adadin mace-mace ba.

Karin bayani: Burkina Faso: Damuwa kan kashe fararen hula

Gwamnatin mulkin soja da kyaftin Ibrahim Traoré ke jagoranta ba ta cika yin magana game da hare-haren da masu kaifin kishi addini ke kaiwa a Burkina Faso ba duk da salwantar rayuka da ake samu. Amma kungiya Acled da ke ba da rahoton wadanda tashe-tashen hankula suka rutsa da su a duniya ta ce  fiye da mutane 26,000 ne suka mutu a hare-hare cikin shekaru tara, ciki har da fiye da 6,000 da aka kashe a wannan shekarar.