Burkina Faso: Tsohuwa ta tsira
August 31, 2022Talla
Cikin watan Afirilun wannan shekara da muke ciki ne dai, 'yan ta'addan suka sace Sister Suellen Tennyson da ke aiki a Congregation of Marianites of the Holy Cross tun daga shekara ta 2014. Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ruwaito cewa Cocin mabiya darikar Katolika ta kasar sanar da cewa, mayakan sun sako ta kuma a yanzu tana tudun mun tsira. Burkina Faso dai, na daga cikin kasashen da ke fama da ayyukan 'yan ta'adda masu ikirarin jihadi a yankin Afirka ta Yamma.