1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan takara 15 a zaben shugaban kasar Nijar

Salissou BoukariJanuary 11, 2016

Ministan cikin gida na Jamhuriyar Nijar ya gabatar da sunayen 'yan takarar shugabancin kasa a zabe mai zuwa na 21 ga watan Febrairu kamar yadda kotu ta yi umarni.

https://p.dw.com/p/1Hb7q
Hoto: Mahaman Kanta

A ranar Asabar ce dai kotun tsarin mulkin kasar ta Nijar wadda nauyin tantance 'yan takara ya rataya a kan ta, ta amince da takarar mutane 15 daga cikin 16 da aka gabatar mata, cikinsu kuwa har da Hama Amadou da a halin yanzu ya ke tsare a gidan kaso na garin Fillingue.

Akwai kuma Abdou Labo da shi ma ake zarginsa da laifin safarar jarirrai, sannan akwai Mahamane Ousmane wanda wata jam'iyya mai sunan MNRD ta tsayar da shi bayan rikicin jam'iyyarsa ta CDS Rahama wadda Abdou Labo ya tsaya a karkashinta. Kotun dai ta yi watsi ne da takarar Abdoul-Karim Bakasso wanda yake shugaba wata karamar jam'iyya bisa dalillan matsalar takardar da ke tantance lafiyar dan takara.

A wannan Litinin din ce kuma kotun a jamhuriyar ta Nijar za ta bada sakamakon ko za ta baiwa Hama Amadou sakin Talala ko akasin hakan.