1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan takara 50 za su ƙalubalanci Paul Biya a zaɓen shugaban ƙasar Kamaru

September 5, 2011

A ranar tara ga watan Oktoba za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Kamaru, inda 'yan takara 50 za su fafata da shugaba mai ci Paul Biya a wannan zaɓe.

https://p.dw.com/p/12TTX
Paul Biya da Benedikt na 16, lokacin ziyarar Paparoman a KamaruHoto: AP

Daga cikinsu kuwa har da John Fru Ndi, mutumin da ya daɗe yana jagorantar 'yan adawa, wanda kuma ya sha kaye a hannun Paul Biya a zaɓen shekarar 2004.

Da yammacin ranar Lahadi shugaban Kamaru Paul Biya wanda ya kwashe shekaru 29 akan mulki ya ƙaddamar da aniyarsa ta tsawaita mulkin na sa a wannan ƙasa da ke yankin tsakiyar Afirka mai man fetir. Wannan mataki da shugaba Biya mai shekaru 78 a duniya ya ɗauka ya kushe duk sukar da ake masa cewa bai kamata ya tsaya takarar zaɓen da ake shirin gudanarwa a ranar 9 ga watan Oktoba ba.

Jami'an jam'iyar CPDM dake jan ragamar mulki a Kamaru suka miƙa takardun neman tsayawa takarar Biya ɗin ga hukumar zaɓen ƙasa wato Elecam. A lokacin da suke miƙa takardun tsayawa takarar, muƙaddashin babban sakataren jam'iyar CPDM Gregoire Owona ya ce shugaba Paul Biya ya amsa kiraye kirayen jama'a ne na sake tsayawa takarar neman shugabancin ƙasar. Shugaban dai zai fuskanci adawa daga 'yan takara kimanin 50 ciki har da John Fru Ndi na babbar jam'yar hamayya ta Socila Democratic Front wato SDF a taƙaice.

Rashin haɗin kan 'yan adawa wata nasara ce ga Biya

Henry Fotso wakilin sashen Faransanci na DW a birnin Duala na Kamaru ya ce Biya ba zai fuskanci wata adawa mai tsanani ba saboda rashin haɗin kan jam'iyun hamayya.

"Haƙiƙanin gaskiya kuma a zahiri a matsayi na na ɗan jarida ba na gani aƙwai wani ɗan takara daga cikin waɗannan 'yan takara masu yawa da zai iya hana Paul Biya sake samun nasarar ɗarewa akan kujerar shugabancin ƙasar Kamaru. Ba za a iya yin dogaro ba da John Frundi wanda shi ma a baya bayan nan ƙwarjinansa ya ragu cewa zai iya samun nasara gaban Paul Biya a zaɓen."

Afrika Kamerun Yaounde
Tsakiyar birnin YaoundeHoto: picture-alliance / maxppp

A shekarar 1998 gwamnatin Paul Biya ta yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar kwaswkarima da nufin cire wa'adin shugabanci domin share masa hanyar sake tsayawa takara, to sai dai 'yan adawa sun dage cewa dole ne yayi aiki da tsohuwar dokar ƙasa ta 1996, wadda a ƙarƙashinta wannan wa'adin na shekara bakwai shi ne na ƙarshe.

Fargabar tashe tashen hankula bayan zaɓe

Manazarta harkokin yau da kullum na fargabar maimaicin tashe tashen hankula shigen waɗanda suka biyo bayan kwaskwarimar da aka yiwa kundin tsarin mulki a shekarar 2008, wanda ya ba wa Biya damar sake tsayawa takara, inda aka kashe mutane fiye 40.

Alyce Kom lauya ce kuma ɗaya daga cikin shugabannin ƙungiyoyin fara hula masu gwagwarmayya, ta nuna cewa suna cikin fargaba na rashin tabbas kan abinda ka iya faruwa a ƙasar.

"Idan ka saurari abinda mutane suke faɗa dangane da wannan mulki na Paul Biya to kam ba za a samu fidda tsamanin wani abu ya biyo bayan zaɓen ba kamar yadda muke ganin irin abubuwan dake faruwa a cikin wasu ƙasashe musamman na Afirka bayan zaɓe."

Mutane miliyan 7.3 aka yiwa rajistar zaɓe idan aka kwatanta da miliyan biyar a shekarar 2004 wanda Biya ya lashe da kusan kashi 71 cikin 100. A cikin watan Yuli majalisar dokokin Kamaru ta amince da wata sabuwar doka da ta ba wa 'yan ƙasar dake ƙatare izinin kaɗa ƙuri'a a zaɓen shugaban ƙasa. Wannan mataki na zaman wani ƙarin matsin lamba ga shugaba Biya.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu