1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zubar da jini na muni a Afganistan

Usman Shehu Usman
November 11, 2018

Mayakan Taliban sun kai hari a wani sansanin sojoji inda suka halaka sojoji 12 kana suka bizne boma-bamai wadanda suka tashi suka halaka shugabannin kabilun yankin hudu lokacin da suka je daukar gawan soji.

https://p.dw.com/p/383sP
Afghanistan Angriffe in Ghasni
Hoto: Getty Images/AFP/Z. Hashimi

Babban jami'in gwamnatin yankin Safder Mohsini, ya bayyana cewa mayakan sun kuma sace sojoji biyu kana suka raunata wasu akalla uku, a wani hari na daban da suka kai. 'Yan Tabaliban sun kona sansanin soji kana suka kewaye shi da bama-babamai. A 'yan kwanakin nan kusan ko wace rana Taliban sai ta kai hari kan jami'an tsaron Afganistan.