'Yan tawaye na gwabza fada a Siriya
July 19, 2017Talla
Barkewar rikici tsakanin kungiyoyin biyu na zuwane kwanaki kalilan bayan da wata kungiyar 'yan tawaye ta kaddamar da kafa tuta a yankin Idlib, an dai kwashe tsawon sa'anni 24 ana fafatawa tsakanin kungiyar jihadi ta Hayat Tahri al-Sham da kungiyar Ahrar al-Sham dake zama kungiyar 'yan tawaye mai karfin iko a yankin Idlib dake arewa maso yammacin kasar.
Kungiyoyin kare hakkin bil'adama a Siriya sun ce wannan ba shi ne karon farko da 'yan tawayen ke gwabzawa da juna ba, tun bayan da suka karbe iko da Idlib. A yanzu dai yankin na Idlib na cikin yankunan da dakarun gwamnatin Bashar al-Assad ke fatan karbe iko da su daga hannun 'yan tawayen Siriya.