1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan tawaye sun fi karfin mahukuntan Libiya

August 26, 2014

Wannan ne fada mafi tsauri a Libiya tun bayan faduwar Gaddafi. Sabuwar majalisar ba ta da karfi, kuma 'yan tawaye na ci gaba da yaki, abin da ke barazana ga daidaituwar siyasar kasar

https://p.dw.com/p/1D1Ul
Abdullah al-Thani Libyen Regierungschef 03.06.2014
Firaminista Abdullah al-Thani.Hoto: AFP/Getty Images

Kasar Libiya, ba ta taba fama da irin tashin hankalin da kasar ta samu kanta a ciki ba, tun daga lokacin faduwar gwamnatin marigayi kanar Gaddafi zuwa yanzu, bisa la'akari da cewa gwamnati da sabuwar zababar majalisar dokokin ba su da iko kan kungiyoyin mayaka da ke ci gaba da gwabza fada tsakaninsu, abin da ke zama wata kasawa ta gwamnatin rikon kwarya kasar.

Shekaru uku bayan faduwar gwamatin kanar Gaddafi, Libiya ta fada cikin wani bala'i wanda da sanu a hankali a kowace rana al'amura ke dada rincabewa tun daga shekarun 2011.

Kungiyoyin mayakan da suka yi taron dangi suka hada kansu a lokacin baya, suka yaki gwamatin kanar khadafi su ne a yanzu suke cin junasu. Kungiyoyin mayakan sun karkasu dabab- daban wadanda suka yi wakance da kuma wadanda suka kuno kai a cikin shekaru biyu na baya baya nan.

Me ke karawa kungiyoyin tawayen karfi?

Misali akwai hadin gwiwa na kugiyoyin Fajir da na Misirata wadanda suka kasance jigo a cikin juyin juya halin da ya share gwamnatin Gaddafi. Sannan akwai kungiyoyin mayakan na Zitane masu ra'ayin balewa dake a yankin gabashi wadanda suka hada da wasu tsofin magoya bayan marigayi Gaddafi wadannan kuniyoyi su ne suke ta shan gumurzu, inda tankokin yaki ke ci gaba da yin barin wuta a kan titi na filin saukar jiragen sama na birnin Tripoli, wanda kusan duk suka lalata gine-ginen da ke a filin fadan da suka kwashe makonni suna yi domin karbar iko da filin saukar jiragen saman wanda a yanzu hadin gwiwar kungiyoyin mayakan Fajir, masu kishi addini suke iko da shi.

Wolfram Lacher wani kwararre a kan kasar ta Libiya da ke a wata cibiya ta binciken kimiyyar siyasa dake a birnin Berlin na Jamus, a cikin wata hira da tashar DW ta yi da shi, ya ce abin da ke faruwa a Libiyar na nuna cewar babu wata gwamnatin da ke da iko a kan hana lalata kadarorin kasar

Libyen Kämpfe am Flughafen
Abin da ya rage a filin jirgin saman LibiyaHoto: Reuters

Filin saukar jiragen sama ta kasa da kasa a cikin hedkwata wata babbar shaida ce ta ikon gwamnati da farko, ya ce yin fada a gewayen fili da ma ciki na nuna cewar, babu wata gwamatin da ke da karfin ikon hana aikin ta'addi na wasu mayakan da ke kokarin lalata filin saukar jiragen sama domin hanawa abokan gaba cin moriya

Masu kishin addinin sun yi watsi da ita suna masu cewar waccan tsohuwar majalisar wadda suke da rinjaye a ciki, ita ce mai halacci kuma a latilas saboda tashin hankalin da ake yi a biranen Tripoli da Beghazi, majalisar ta koma da zama a birnin Tobruk da ke a yankin gabashi, yayin da dubban jama'a ke yin hijira daga Libiyar zuwa Tunisiya da sauran kasashe domin samun mafaka, kuma jami'an diplomasiyya da dama sun ficce daga kasar.

Mawallafa: Allmeling Anne/Abdourahamane Hassane
Edita: Pinado Abdu Waba