1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan tawayen Mali sun ayyana 'yancin Azawad

April 6, 2012

MNLA da ke cikin jerin ƙungiyoyin 'yan tawaye da suka karɓe ikon biranen arewacin Mali sun yi ikiƙirarin ɓallewa tare da kafa ƙasar Azawad mai cin gashin kanta.

https://p.dw.com/p/14Yqq
A Tuareg nomad stands near a 13th century mosque in Timbuktu in this March 19, 2004 file photo. Just as Timbuktu with its exotic staccato name is part of the lore of the Sahara, this same mystery cloaks the Tuaregs, those blue-robed desert marauders who have peopled adventure stories and Hollywood films for years. But there is nothing fictional about the rebels of the National Movement for the Liberation of Azawad (MNLA) who charged into Timbuktu on Sunday to plant their yellow, green, red and black flag in the city to claim it as part of a homeland covering an area of northern Mali the size of France. To match story MALI-TIMBUKTU/MYTH REUTERS/Luc Gnago/Files (MALI - Tags: POLITICS CIVIL UNREST RELIGION)
Masallacin Tombouktou ma ya faɗa hannun 'yan tawayeHoto: Reuters

Ƙungiyar MNLA ta 'yan tawayen Mali ta ayyana yankin arewacin ƙasar a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta. Cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafin internet, da kuma wata hira da wani kakakinta main suna Mossa Ag Attaher ya yi da tashar telebijin ta France 24, ƙungiyar ta ce ta raɗa wa sabuwar ƙasar ta Abzunawa zalla suna Azawad. Tun a ranar alhamis ne dai, 'yan tawayen na Mali suka tsagaita buɗe wuta, sakamakon kame birane kidal da Gao da kuma Tombouctou da ke da mahimmaci a garesu da suka yi nasara yi.

Wannan ya zo ne a daidai lokacin da ƙungiyar Amnesty International ta yi gargadi game da mummmunan halin da 'yan Mali za suka sami kansu a ciki idan ba a kai musu agajin cikin gaggawa ba. Ƙungiyar da ke da cibiyarta a birnin London ta ce duk da cewa abzunawa 'yan tawaye sun yi iƙirarin tsagaita buɗe wuta, amma kuma 'yan Mali na cikin barazanar faɗawa cikin halin na taɓarɓarewar rayuwa.

A cewar ƙungiyar dai, rikici na tawaye da kuma juyin mulki sun daɗa jefa ƙasar ta yammacin Afirka cikin halin na koma baya da kuma ƙarancin abinci. Ƙungiyoyin agaji sun ƙaurace wa Mali tun bayan da ƙasar ta tsinci kanta cikin tagwayen rikice rikice. Ƙungiyar agaji ta Oxfam ga misali ta bayyana cewar a halin yanzu 'yan Mali miliyon uku da dubu 500 na fiskantar karancin abinci.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: zainab Mohammed Abubakar