1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan tawayen Mali sun kashe gomman mayakan Wagner

August 2, 2024

'Yan tawaye a arewacin Mali sun kashe gomman mayakan sojojin hayan Rasha na Wagner da kuma dakarun gwamnati a kusa da iyakar kasar da Aljeriya a karshen watan Yuli.

https://p.dw.com/p/4j2qo
Hoto: Nicolas Remene/Le Pictorium/imago images

A ranar Alhamis ne 'yan tawayen na Taureg suka ce sun kashe mayakan Wagner 84 da kuma sojojin Mali 25 a sansanin soji da ke Tinzaouatene. 'Yan tawayen Abzinawa masu rajin kafa kasa mai suna Azawad, sun ce wasu mayakan 30 suka jikkata ko ma suka mutu an kai su yankin Kidal.

Karin bayani: Sojojin Mali na matsa lamba wa 'Yan Tawayen Azawad

Masu neman ballewar sun ce sun yi garkuwa da wasu dakarun, inda su ma suka rasa mayakansu tara yayin musayar wuta. Masu sharhi dai sun alakanta fadan na wannan lokacin da gagarumin asarar dakaru mafi girma da Wagner ya yi a nahiyar Afirka.

Ko a ranar Alhamis, wani harin jirage marasa matuka na ramuwar gayya da 'yan tawayen suka kai ya yi sanadin rayukan 'yan kasashen Nijar da Sudan da kuma Chadi, kana suka gargadi kasar Burkina Faso da kada ta shiga fadan da babu ruwanta.