1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan tawayen Siriya na barazanar kaurace wa tattaunawar

Salissou Boukari
January 3, 2017

Cikin wata sanarwa da suka fitar, hadin gwiwar kungiyoyin 'yan tawayen Siriya akalla 10, sun yi barazar kin halartar zaman tattautanwar da za a yi a karshen watan Janairu a birnin Astana na kasar Kazakhstan.

https://p.dw.com/p/2VCGk
Syrien Damaskus Wasserkrise IS blockiert Wadi Barada
Hoto: picture-alliance/dpa/Y. Badawi

'Yan tawayen dai sun yi wannan barazana ce, dangane da abun da suka kira kin mutunta yarjejeniyar daga bangaran dakarun Gwamnatin Shugaba Bahar Al-assad. Su dai 'yan tawayen sun ce sun yi biyayya ga yarjejeniya, amma kuma bangaran dakarun gwamnati da masu mara musu baya, na ci gaba da take taka ta musamman ma a yankunan Wadi Barada da kuma Ghouta ta Gabas da dukanninsu ke cikin jihar Damaskus babban birnin kasar ta Siriya.

A cewar kungiyar da ke sa ido kan kare hakin bil -Adama a kasar ta Siriya, dakarun gwamnati da mayakan Hezbollah 'yan Shi'a na kasar Lebanon da ke mara musu baya, sun ci gaba a wannan Talata da samaman da suke kai wa a yankunan da ke a nisan km 15 da birnin na Damaskus.